Kaduna Electric ta ya yanke wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KEDCO) ya yanke lantarkin gidan gwamnatin Kaduna saboda bashin sama da Naira biliyan 2.9 da yake bi.
Kamfanin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen sadarwa na kamfanin Abdulazeez Abdullahi, ya ce gidan gwamnati bai biya kudin wutar da aka ci ba cikin watanni bakwai.
Idan ba a manta ba a safiyar ranar Juma’a ne gwamnatin jihar ta hannun hukumarta ta haraji, hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe kanfanin wutar lantarkin dake bin sama da naira miliyan 600 na haraji.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wani gagarumin yunkuri da ke nuna yadda ake samun takun saka tsakanin masu samar da wutar lantarki da gwamnatocin Jihohi, kamfanin Kaduna Electric ya yanke wutar lantarki a gidan gwamnatin jihar Kaduna da sauran asusun gwamnatin jihar saboda rashin biyansu kudi.
Kamfanin na Kaduna Electric ya sanar da katse huldar ne bayan kokarin da aka yi na magance matsalar ta hanyar tuntubar juna da sulhu a tsakanin su.
Ya ce duk da biyan Naira miliyan 256 da aka yi a kwanakin baya na wutar lantarki da ake amfani da su a tsakanin Satumba 2023 zuwa Disamba 2023, bashin da gwamnatin Jihar Kaduna ta biya ya ci gaba da yawa, wannan bai kai a cire ba.
Matakin da kamfanin Kaduna Electric ya dauka na yanke wutar lantarkin ya biyo bayan kokarin da aka yi na shawo kan matsalar biyan kudin, ciki har da tuntubar jami’an jihar da dama. Sabanin haka, sauran jihohin da ke karkashin kamfanin Kaduna Electric, wato Sokoto, Kebbi, da Zamfara, sun ci gaba da kula da asusunsu yadda ya kamata, tare da biyan bukatunsu na biyan kudin wutar lantarki da sauran hakkokinsu na biyan wutar lantarki da Kaduna Electric.