Kada a yi amfani da ku wajen lalata Kano, Sarki Sanusi ya fadawa masu zanga-zanga
Mai martaba Sarkin Kano na 16,Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’umma da kada su bari a yi amfani da su a yi barna a Kano da Arewa da ma kasa baki daya.
Sarkin ya yi wannan kirane lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake gidan sarki na cikin garin kano.
Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu zanga-zangar suka sake haduwa a Tudun Wada da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano, a yammacin ranar Juma’a.
Sun sake haduwa bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sassauta dokar hana fita domin ba musulmi damar gudanar da Juma'a.
Da yawa daga cikinsu na rike da alluna yayin da wasu ke rera waka da tafawa yayin da suke tafiya bayan wani matashi ya yi musu jawabi.
A lokacin da yake tattaunawa da manema labaran a yammacin Juma’a, sarkin ya nuna matukar damuwarsa kan yadda aka wawure dukiyoyin jama’a da na wayanda basuji ba basu gani ba, sakamakon zanga-zangar da aka ce za'a da gudanar cikin lumana don nuna adawa da yunwa da kuncin rayuwa a kasar.
Sarkin ya ce abin da ya faru koma baya ne ga jihar da yankin arewa da ma kasa baki daya.
Ya ce, “Yau rana ce ta bakin ciki ga al’ummar Kano yayin da muke tunani kan abubuwan da suka faru a jiya. Rikicin na jiya shi ne abin da masana da shugabanni suka yi ta gargadi kan yiwuwar zanga-zangar lumana tare da yin amfani da wannan damar wajen haifar da tarzoma wanda ya kai ga hasarar rayuka da lalata dukiyoyi da jikkata mutane da dama.
Kamar yadda muka fada yayin taron masu ruwa da tsaki, duk wani tashin hankali a Kano yana cutar da mutane wanda basu da laifi. Matasan da suka mutu ‘ya’yanmu ne, dukiyar da aka kona aka sace ta mutanen Kano ce.An lalata kayan gwamnati kuma kudin al'umma za a dauka domin siyan wasu kayayyakin don haka babu wani abu da wannan abu ya haifar in ba koma baya ba.