Jam'iyyar PDP ta nemi Tinubu ya sake duba manufofi gwamnatin sa

Jam'iyyar PDP ta nemi Tinubu ya sake duba manufofi gwamnatin sa

Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da ta gaggauta sake duba duk wasu manufofinta da tsare-tsare daya dagula rayuwar kasar nan.


Jam’iyyar ta ce jam’iyyar APC ta jefa Nijeriya cikin mawuyacin hali, ta kuma bukaci shugaba Tinubu ya yi wa al’ummar kasar jawabi kan hanyar da za a bi wajen shawo kan lamarin.


Jam’iyyar adawar ta yi nuni da cewa zanga-zangar da ‘yan Nijeriya suka yi a fadin kasar ba za ta faru ba idan da a ce gwamnatin APC ta nuna gaskiya da jajircewa wajen magance wahalhalun da ke faruwa a halin yanzu sakamakon rashin aiwatar da ingantattun manufofi.



Sakataren yada labaran PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana cewa, “Yan Nijeriya za su iya tunawa cewa jam’iyyar PDP a lokuta da dama ta ba gwamnati shawarwari kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Abin baƙin ciki, waɗannan shawarwari ba su samu karbuwa ba,wanda hakan yasa ake halin da ake ciki yanzu

1 Comments

  1. Tinubu Baya ji kokadan Bai dace kana jagoran tar al umaba ace kana wasa da kukan su shi kudin da ake so ya maida fa natalakane ,sai maganar tsaro wallahi da Jami an tsaro da gaske sukai da bahakaba

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp