Jami’anmu ba su yi harbi da harsashi mai rai ba a lokacin zanga-zanga – IGP

 Jami’anmu ba su yi harbi a lokacin zanga-zanga ba – IGP

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya ce babu jami’insu da ya yi harbi a lokacin zanga-zanga.


Sufeton ya bayyana haka ne a lokacin ya ke jawabi a taron shugabanin tsaro a ranar Talatar,a Abuja lokacin da yake kare zargin da aka yi wa jami’ansu na yin harbi a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a Nijeriya.


Ya ce duk jami’in da aka gani da bakin kaya a ranar zanga-zanga ba jami’insu ba ne saboda ba kayan da suka saba sanyawa suka sa ba a ranar.


Sannan ya ce,sun kama masu dinka tutocin kasashen waje don su kai su wajen masu daukar nauyinsu.


Ko a jihar Kano 'yan sanda sun fara gurfanar da wa'yanda ake zargi da tayar da tarzoma tare da bannata dukiyoyin al'umma a yayin zanga -zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post