Iyayen matashi dan shekara 25 da aka harbe yayin zanga-zanga a Kano sun nemi a yi musu adalci


Iyayen matashi dan shekara 25 da aka harbe yayin zanga-zanga a Kano sun nemi a yi musu adalci


Daya daga cikin iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a zanga-zangar da aka yi a Kano a makon jiya ta bukaci a yi musu adalci.


Akalla mutane takwas ne aka ruwaito an sun rasa rayukansu a rikicin da ya barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a yankin Rijiyar Lemo da Kurna Asabe da ke karamar hukumar Fagge a ranar Asabar.


Bashir Muhammad Lawan mai shekaru 25 yana daga cikin wadanda aka kashe a lokacin da masu zanga-zanga a Rijiyar Lemo da ke kan titin Katsina suka yi artabu da 'yan sanda.


Iyalan marigayi Bashir, suna alhinin rasuwarsa, sun shaida wa Daily Trust cewa an kashe dansu ne a lokacin da yake fafutukar kwato hakkinsa a matsayinsa na dan Najeriya.


Malam Muhammad Lawal, mahaifin Bashir, ya ba da labarin cewa an kashe dansa mintuna sha biyar kacal da barin gida don shiga zanga-zanga.


Ya kara da cewa wasu matasa da dama da suka hada da mata da kananan yara ne ake zargin ‘yan sanda sun harbe su a ranar.


A cewar wasu ‘yan uwan mamacin, ‘yan sandan sun fara harbin harsashi ne a lokacin da gungun masu zanga-zangar suka fara yi musu ihu suna cewa bamayi.



Khadija Bala, kanwar Bashir, ta ce yana gudu ne domin ya fake da harbin bindiga ya same shi.


Khadeejah tace sun yi zanga-zangar ne kawai amma an ce musu 'yan daba,don haka muna son a yi masa adalci.


Duk da cewa gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga amma a ranar Litininin an samu wasu matasa na zanga -zangar dauke da tutar kasar Russia.


Sai dai gwamnatin jihar ta sanar da cewa an kama wasu mutane 632 da ake zargi da wawure dukiyar jama'a a yayin zanga-zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post