Babban sufeton 'yan sandan Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce zanga-zanga da aka gudanar a ranar Alhamis, ta yi sanadiyyar mutuwar dan sanda da raunata da dama.
Kazalika, IGP Egbetokun ya ce zanga-zangar ta kuma yi sanadiyyar lalata ofisoshin 'yan sanda a sassan kasar.
A taron manema labarai a daren Alhamis a Abuja, IGP Kayode Egbetokun bai ce uffan ba game da zargin kisan fararen hula a yayin zanga-zangar ba a fadin kasar.