Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai fice daga jam’iyyar PDP ba duk da rikicin cikin gida da ake fama da shi.
Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a yayin wani taron manema labarai domin cika shekara guda a kan mukamin sa.
Matakin na Wike ya zo ne a daidai lokacin da ake gwabza fada na neman mulkin jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas.
Category
Labarai