Hukumar zaben Kano ta kayyade kudaden tsayawa takara



Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano ta bukaci ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi su biya naira miliyan 10, Kansiloli za su biya miliyan 5 a matsayin kudin fom na tsayawa takara wanda za'a gudanar ranar 30 ga watan Nuwamba a jihar.

Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ne ya bayyana haka yayin gabatar da ka’idojin zabe da jadawalin zaben ga wakilan jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa dan takarar da ke neman kujerar shugabancin karamar hukuma dole ne ya biya Naira miliyan 10 domin samun cancantar shiga zaben, yayin da dan takarar kansila zai biya Naira miliyan 5.

Malumfashi ya bayyana cewa ka’idojin sun fayyace duk batutuwan cancanta da rashin cancantar ‘yan takara.

1 Comments

  1. 𝐆𝐚𝐬𝐤𝐢𝐲𝐚 𝐧𝐢 𝐚𝐧𝐚𝐰𝐚 𝐫𝐚,𝐚𝐲𝐢𝐧,𝐚𝐧𝐲𝐢 𝐡𝐚𝐤𝐚𝐧𝐞 𝐝𝐚𝐧 𝐧𝐞𝐬𝐚𝐧𝐭𝐚 𝐭𝐚𝐥𝐚𝐤𝐚 𝐤𝐮𝐬𝐚𝐧 𝐭𝐚𝐫 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐦𝐢𝐥𝐤𝐢,𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚𝐧𝐝𝐚 𝐲𝐚𝐡𝐚𝐮 𝐛𝐚 𝐚𝐝𝐚𝐥𝐜𝐢 𝐳𝐚𝐢𝐲𝐢𝐛𝐚,𝐬𝐚𝐢 𝐲𝐚𝐠𝐚 𝐲𝐚𝐜𝐢 𝐫𝐢𝐛𝐚𝐫 𝐚𝐛𝐢𝐧 𝐝𝐚 𝐲𝐚𝐤𝐚𝐬𝐡𝐞.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post