Hukumar karbar korafe-korafe za ta gudanar da bincike kan zargin badakalar wasu kudade a Kano
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, PCACC, ta kaddamar da fara bincike a kan zargin karkatar da wasu makudan kudade, da kuma zargin an karkatar da kudaden tallafi na gwamnatin tarayya.
Daga cikin wadanda ake sa ran za a yi musu tambayoyi kan badakalar da ake zargin sun hada da Musa Garba Kwankwaso, wanda dan gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne da kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Shehu Wada Sagagi.
Musa Kwankwaso, wanda dan uwan kwankwaso ne ubangidan Abba Kabir Yusuf, an yi zargin cewa yana da hannu a badakalar sayen kayayyaki. Wani kamfani mai suna Novomed Pharmaceuticals, wanda Musa Kwankwaso darakta ne kuma ake kyautata zaton mallakarsa ne ya bayar da kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwangilar da aka ce an bayar da ita ba tare da bin ka’ida ba, ta kunshi kowace karamar hukuma tana biyan kusan Naira miliyan 9 duk wata, wanda ya kai Naira miliyan 396 a duk wata.
Wannan badakalar ta fito fili ne a lokacin da Bello Galadanchi, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta umurci kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 44 da su biya kimanin Naira miliyan 10 domin samar da maganin, tare da bayar da kwangilar ne kadai ga kananan hukumomin. Novomed Pharmaceuticals.
A karshen makon da ya gabata ne Gwamna Abba kabir Yusuf ya nesanta kansa da kwangilar inda ya musanta sanin tun da farko kan yarjejeniyar tare da bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.
A wata tattaunawa ta musamman da Daily Trust,shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji ya ce sun gayyaci duk wa'yanda ake zargi domin amsa tambayoyi tare da gano gaskiyar lamarin.
Ya bayyana cewa gayyatar na daga cikin kashi na farko na binciken da nufin tattara muhimman bayanai da takardu da suka shafi kwangilar.