Haryanzu jihohi ba su karbi Naira biliyan 570 daga gwamnatin tarayya - Gwamna Seyi

 


Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce jiharsa ba ta amshi Naira Biliyan N570bn da Gwamnatin Tarayya ta ba jihohi domin yaki da yunwa kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito

A yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin kasar Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta biya ₦570bn ga jihohi 36.

Makinde ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Alhamis, ya ce jihar ba ta da masaniyar irin wannan tallafin.

Makinde shi ne gwamna na biyu daga jam’iyyar PDP da ya caccaki shugaba Tinubu kan jawabin sa.

Post a Comment

Previous Post Next Post