Har yanzu shugaban Amurka yana amfani da jirgin sama da yayi shekaru 34 amma Nijeriya ta yi watsi da jirgin mai shekaru 19
Bayan na makonni fadar bata ce komi ba, kan batun siyan jirgin shugaban kasar ta bayyana siyan sabon jirgin kirar Airbus A330, a ranar Litinin din da ta gabata.
Tattaunawa game da sabon jirgin shugaban kasar ya fara ne bayan matsalolin da jirgin Boeing Business Jet (BBJ) ya samu a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shekaru 19 da suka gabata ya samu matsala a wata tafiya da yayi Saudiyya da Netherlands da kuma Afirka ta Kudu.
Sai dai shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da jirgin saman haya, lamarin da fadar shugaban kasar ta bayyana a matsayin abin kunya.
Yayin da jami’an gwamnati ke ta cece-ku-ce kan samar da wani sabon jirgin, talakawa sun nuna rashin amincewar su, ganin yadda matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da ke addabar Nijeriya.
Sai dai a watan Yuni, wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Nijeriya ta sayi jirgin Airbus A330 daga wani bankin kasar Jamus. Rahotanni sun bayyana cewa bankin ya kwace jirgin ne daga hannun wani basarake da ba a bayyana sunansa ba wanda ya ki biyan bashi.
Fadar shugaban kasar dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, lamarin da ya bar jama’a cikin duhu game da sayan jirgin. A yayin da ake ta cece-kuce a kan kamfanin saga na kasar Sin, ‘yan Nijeriya sun samu labarin cewa da gaske an sayi sabon jirgin. Amma duk da haka fadar shugaban kasar ta yi shiru har zuwa ranar Litinin lokacin da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar da hotuna tare da bayanai
Onanuga, wanda bai bayyana kudin sabon jirgin ba, ya ce, sabon jirgin da aka sayo bai yi wani tsada ba, kuma ya ceci Nijeriya da makudan kudaden da ake kashewa da kuma kudin man fetur.