Hadin kai tsakanin hukumonin tsaro tare da masu ruwa da tsaki nada matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro-Christoper Musa

Hadin kai tsakanin hukumonin tsaro tare da masu ruwa da tsaki nada matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro-Christoper Musa

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce rundunar soji na ci gaba da wayar da kan sojoji kan hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin kare makarantu daga hare-hare.


Ya bayyana haka ne a yayin bude taron kwana biyu kan makarantun tsaro a hedikwatar runduna ta daya ta sojojin Nijeriya dake Kaduna, CDS ya jaddada muhimmancin samar da muhimman abubuwa kamar babura da na’urorin sadarwa domin isa makarantu cikin hanzari a lokacin da ake bukata.


Wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Emeka Onumajuru, ya ce, “Rundunar Sojin Nijeriya ta ‘yan Nijeriya ce kuma za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kare al'umma, tare da yin aiki da dukkanin hukumomin tsaro.


Babban kwamandan rundunar soji ta daya (GOC), Manjo Janar Mayirenso Saraso, ya kuma yi kira da a hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaro a makarantun jihar.


Kwamishinan tsaro na harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce tsakanin watan Yulin 2021 zuwa Maris 2024, jihar Kaduna ta fuskanci sace yara ‘yan makaranta da dama.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp