Hukumar kula da Almajirai da yaran da ba su zuwa makarantun boko a Nijeriya ta sanar da kammala zakulo yara sama da 20,000 domin mayar da su makarantun boko.
An samu wannan jimillar yaran ne bayan wani gagarumin aikin fadakar da jama'a na makonni uku da jami'an hukumar NCAOOSCE suka shiga lunguna da sako-sako na babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban hukumar Muhammad Sani Idris ya jinjina wa jami'ansa da ake kira Marshals wadanda aka dora wa alhakin zakulo yaran da ba su zuwa makarantun bokon cikin wani kankanin lokaci.
A cikin wata sanarwa da Malam Nura Muhammad, babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga shugaban hukumar ta NCAOOSCE ya fitar, hukumar ta ce tana da shirin saka milyoyin yara makaranta a duk shekara.
Sanarwar ta ce, da farko an fara kokarin ganin an saka yara 10,000 makaranta, amma irin hobbasar da hukumar ta nuna ya sa aka samu sakamakon da ya ba mutane mamaki.
Muhammad Sani Idris ya ce nan da zuwa watan Satumba, wadannan yara da ake zakulo za a sanya su a makarantun boko dabam-dam da ke yankin Abuja. Ana kuma sa ran daga nan shirin zai fadada zuwa suaran yankunan Nijeriya.