Gwamnatin tarayya za ta zauna da kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU a yau kan batun shiga yajin aiki
A yau ne wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, za su gana da jami’an kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da sauran masu ruwa da tsaki domin warware batutuwan da suka shafi kowane bangare.
Hakan ya biyo bayan barazanar da ASUU ta yi na shiga yajin aikin a baya-bayan nan bayan fitar da sanarwar kwanaki 21 ga gwamnatin tarayya kan wasu batutuwa da ba a warware ba.
An bayar da sanarwar ne a karshen taron kungiyar ASUU ta kasa (NEC), wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan, kuma an mika kwafin ga ma’aikatun kwadago da ilimi na tarayya.
Wasu daga cikin batutuwan sun hada da asusun farfado da jami'o'in gwamnati na gaggawa; biyan alawus-alawus na ilimi; da kuma sakin albashin da aka hana, basussukan karin girma, IPPIS da cire wasu mambobi da sauran su.
Yajin aikin karshe da kungiyar ASUU ta shiga a lokacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shafe sama da watanni takwas ana gudanar da harkokin ilimi a fadin kasar nan.
Ministan ilimi ya shaida wa manema labarai, a wani taron manema labarai na cika shekara guda na gwamnatin, a karshen mako a Abuja, cewa an aike da wasikun gayyata ga jami’an ASUU da wasu kungiyoyi da dama da za su zauna a taron.