Gwamnatin tarayya tayi kira ga ma'aikata da su yi rijistar sayen shinkafar da za ta sayar mai nauyin 50kg akan kudi dubu 40,000
Gwamnatin tarayya tace ta kammala shirin sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 a kan Naira 40,000 ga ma’aikatan gwamnati da nufin magance matsalar karancin abinci da ke addabar al'ummar kasar.
A wata wasika daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin tarayya mai dauke da sa hannun daraktan ma’aikatar, Jaiyesimi Abimbola, ta sanar da hakan.
An bayyana cewa za a gudanar da biyan kudin da kuma rabon shinkafar ne ta ofisoshin da aka kebe yayin da shugaban kungiyar hadin gwiwa na ma’aikatar zai kasance mai sa ido kan yadda ayyukan zasu kasance
Sanarwar tace a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin an shawo kan matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar nan, an umurce ni da in sanar da ku cewa, za a sayar da buhunan shinkafa 50kg a kan kudi naira 40,000 kacal a kan kowane buhu ga ma'aikatan gwamnati masu bukata.
An sanar da cewa, ana buƙatar duk ma'aikatan da ke da sha'awar su cika fom na Google akan gidan yanar gizon OHCSF, https://www.ohcsf.gov.ng, buga, kuma a mika su ga Darakta, HR, don amincewa.
A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta ce ta samar da cibiyoyi a fadin kasar nan inda ‘yan Nijeriya za su iya siyan buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan Naira 40,000.
Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma na kasa, Muhammed Idris, ya ce shirin na daya daga cikin wasu tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ta yi na saukaka yanayin rayuwa ga ‘yan kasa.
Shegiyar gomnati wacce bata da uba. Sauran yan kasar fa?
ReplyDeleteAykin banza. Iya maikata za’a siyarwa.
ReplyDeleteShin kowane ma aikaci kona federal government kadai
ReplyDeleteShashancin banza kawae
ReplyDeleteMuda bamu aikin gwamnati fah
ReplyDelete