Gwamnatin tarayya ta amince da tallafin wutar lantarki da kashi 50% ga asibitocin gwamnati a fadin kasar.
Karamin ministan lafiya da walwalar jama'a Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a jihar Kaduna yayin wata ziyarar aiki.
Yace wannan dai na da nufin rage kudaden tafiyar da asibitocin gwamnati.