Gwamnatin tarayya ta ce ta kafa aƙalla wuraren kula da tsofaffi guda 40 da aka tanadar musamman don kula da tsofaffi a cikin Ma’aikatu, Sassa da Hukumomi daban-daban guda 40, tana mai cewa ba za a iya barin wata hukuma ko ma’aikata guda ɗaya ta rike dukkan al’amuran da suka shafi tsufa ba.
Duk da cewa gwamnati ba ta bayyana jerin ma’aikatun da aka kafa wadannan sashen ba, amma ta yi gargaɗi kan nuna wariya da ƙyamar tsofaffi a sassa daban-daban, tana mai cewa tsufa abu mai kyau da ya kamata a daraja, ba a raina ba.
Shugabar cibiyar kula da tsofaffi ta kasa (NSCC), Dr Emem Omokaro, ce ta bayyana wannan an Abuja yayin wani taron horarwa na farko don tabbatar kwarewar a bangaren kula da tsofaffi.