A kokarinta na gyaran karatun allo da kuma kawo karshen matsalar rashin zuwa makaranta a Najeriya, Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Sa zuwa Makaranta ta shirya taron bita domin lalubo hanyoyin da za a inganta al’almura.
A dalilin haka ne take kira ga duk wanda ke da wadansu shawarwari a kan matakan da ya kamata a dauka domin cimma nasara, da ya turo bayanan nasa ta email zuwa : info@encaoosce.gov.ng
Domin karin bayani, za a iya kiran wannan lambar: 0909 107 4800.
Mu hada karfi da karfe domin ganin cewa kowanne yaro a Najeriya ya samu ingantaccen Ilimi.
Sanarwa daga: Dr Muhammad Sani Idris, Shugaban Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta