Gwamnatin Nijeriya ta ba wa ‘yan kasuwa wa'adin wata daya su sauko da farashin kayan masarufi



Hukumar kare haƙƙin masu sayen kayayyaki a Nijeriya FCCPC ta ba ‘yan kasuwa masu tsawwala farashin su wa’adin wata guda su gaggauta karya farashin kayan su. 

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Sabon shugaban hukumar, Tunji Bello, a wajen wani taron kwana daya na masu ruwa da tsaki suka yi kan ƙazamar ribar ‘yan kasuwa ke samu a Abuja.

A cewar Bello, taron an yi shi ne don magance karuwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post