Mun shirya biyan N70,000 mafi karancin albashi - Gwamnatin jihar Nasarawa

Mun shirya biyan N70,000 mafi karancin albashi - Gwamnatin jihar Nasarawa

Gwamnatin Nasarawa ta ce a shirye take ta biya sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar.

Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin al'umma Peter Ahemba ne ya bayyana haka a ranar Talatar a Lafia, babban birnin jihar a lokacin da ya ziyarci ofishin kungiyar ‘yan jarida da ke jihar.

Ya ce biyan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati ba wai kawai zai inganta jin dadin su ba ne har ma zai kara musu kwarin gwiwar gudanar da ayyuka.

A kan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar, mai taimaka wa gwamnan ya yi kira ga al’ummar kasar da su kawo karshen zanga-zangar da kuma bin tafarkin zaman lafiya ganin cewa tuni gwamnati ta dauki matakin magance wasu korafe-korafensu.

Yace tsarin mulki ya tanadi ‘yan kasa su yi amfani da ra’ayoyinsu ta hanyar zanga-zangar lumana.

Ahemba ya bayyana cewa babu wata gagarumar zanga-zanga a jihar Nasarawa sakamakon kyawawan manufofi da tsare-tsare da Gwamna Abdullahi Sule ya yi na magance wahalhalun da al’ummar jihar ke fuskanta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp