Gwamnatin jihar Katsina za ta zuba Naira Biliyan N30bn a fannin noma
A ci gaba da kokarin da take yi na bunkasa ayyukan noma don samar da abinci da tattalin arzikin karkara, gwamnatin jihar Katsina ta ce tana shirin zuba sama da Naira biliyan 30 kan harkar noma.
Gwamnan jihar, Mallam Dikko Umar Radda ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan dawowarsa daga hutun wata daya.
Radda wanda ya tafi kasar Sin a karshen hutun da ya yi don duba hanyoyin daidaita harkokin noma a jiharsa, ya ce za a yi amfani da wani bangare na kudaden ne wajen kafa cibiyoyin sarrafa kayan gona a kowace karamar hukuma.
Ya ce cibiyoyin za su horar da manoma dabarun noma na zamani tare da samar musu da kayan aikin noma, ta yadda manyan manoma da kananan manoma za su samu damar yin amfani da kayan aiki daidai gwargwado.