Farashin kayan abinci ya fara sauka a sassan Nijeriya


Har yanzu masara ba ta sauko ba a kasuwar Mai'adua jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya, inda ake sai da buhun masarar ₦95,000, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦90,000 cif .

Sai dai a kasuwannin jihohin Adamawa da Lagos an sai da buhun kan kuɗi ₦90,000 daidai a satin nan, amma a makon jiya farashin ya sha bamban a kasuwannin, inda a jihar Adamawa aka sayar da buhun ₦85,000 a makon da ya shude, sai kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos aka sayar ₦103,000.

To a Kanon Dabo ana sai da buhun masara ₦84,000 a satin na da ke shirin karewa, amma satin da ya wuce ₦87,000 aka sayar da buhunsa, an samu ragin ₦3000 kenan a mako guda.

Farashin masara bai sauya zani ba a kasuwar Giwa jihar Kaduna da aka sayar ₦88,000 a makon da ya gabata, haka ake sayarwa a makon nan.

Ita kuwa Shinkafar Hausa ta fi tsada a kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan satin da ake sayarwa ₦170,000, amma a satin da ya gabata ₦160,000 ne kuɗin buhun Shinkafa a kasuwar.

Sai dai a kasuwar Dawanau jihar Kano farashin bai sauya ba da na makon jiya da aka sai da ₦160,000 daidai.

Haka zalika a kasuwar Mai'adua jihar Katsina farashin buhun Shinkafa 'yar gida bai canza ba da na satin da ya shuɗe, wanda aka saya kan kuɗi ₦145,000.

A kasuwar Mile 12 International Market Lagos an samu sauƙin ₦5000 kan farashin shinkafa da aka sayar ₦150,000 a makon jiya, yayin da ake sayarwa ₦145,000 a makon nan.

Ita ma dai jihar Adamawa farashin bai sauya tufafi ba a kasuwannin da ake saidawa ₦148,000.

A ɓangaren shinkafar Bature kuwa, ta fi tsada a kasuwar Dawanau jihar Kano da ake sayarwa ₦92,000, haka nan a makon da ya gabata ma shinkafar ta fi tsada a jihar da aka sayar ₦98,000.

Shinkafar waje ta fi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagos wanda aka sayar ₦75,000 a satin nan, amma a makon jiya ₦76,000 ake sai da buhun.

Ana sayar da Shinkafar waje ₦87,000 a kasuwannin jihohin Katsina da Kaduna da ke arewacin Najeriya a wannan mako, amma dai farashin ya banbanta a makon da ya gabata, inda a kasuwar Giwa jihar Kaduna ake sayarwa ₦85,000, sai Mai'adua jihar Katsina ake sayarwa ₦88,000-₦90,000.

Sai jihar Adamawa ana sayen buhun Shinkafar Bature ₦78,000-₦80,000 a satin nan.

Ga ma'abota cin alala da kosai kuwa ₦200,000 daidai ake sai da buhun farin wake a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Lagas, yayin da a makon da ya gabata aka sai da ₦220,000, an samu ragin ₦20,000 a makon nan da ke dab da ƙarewa.

A kasuwannin jihar Adamawa ana sai da buhun wake ₦170,180,-190,000 a satin nan, haka aka sai da satin da ya shuɗe.

To a jihohin Kano da Kaduna da ma Katsina, ana sayar da buhun wake ₦170,000 a wannan mako, farashin haka yake a makon da ya gabata a kasuwannin jihohin Kaduna da Katsina, sai dai kuma a jihar Kano farashin waken ₦155,000 ne a makon da ya gabata.

Bari mu kammala farashin kayan abinci na wannan sati da farashin taliyar Spaghetti.

Kwalin taliyar ya fi tsada a kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da ake saidawa ₦19,500, bayan da a makon jiya aka sayar ₦18,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano,sai Giwa jihar Kaduna aka sayar ₦19,000.

A kasuwar Mile 12 International Market Lagos ma farashin bai canza ba dana makon jiya, wanda aka sayar ₦19,000.

₦17,400 aka sayi kwalin taliya a kasuwar Mai'adua jihar Katsina a makon nan, bayan da a makon da ya shude aka saya ₦17,600.

To kasuwar zamani da ke jihar Adamawa ₦17,700 ake sayar da kwalinta a makon daya gabata, amma a makon nan ₦17,300 ne kuɗin kwalin taliyar.

Alƙaluman da hukumar kididdiga ta kasa ( NBS) ta fitar a watan Yulin 2024 ya nuna cewar hauhawar farashin kayayyakin masarufi ya yi kasa da kaso 33.40, saɓanin na watan Yuni da kaso 34.19.

DCL Hausa A'isha Usman Gebi.

Post a Comment

Previous Post Next Post