Fada ya kaure tsakanin wasu direbobi da manajojin Dangote a Obajana

Wasu bayanai da DCL Hausa ta samu na cewa wani hargitsi ya kaure tsakanin wasu direbobin motocin kamfanin Dangote da ke kamfanin na Obajana a jihar Kogi da wasu manajojin kamfanin.

Majiyar DCL Hausa da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce rikicin har ya yi sanadiyyar ji wa wasu daga cikin manajojin raunuka munana.

"Da idona, na ga an karya manaja daya, amma wasu abokan aikina sun ce wadanda aka karya sun fi mutum daya", in ji majiyar.

Wannan rikici dai na zuwa ne a daidai lokacin da direbobin motocin kamfanin na Dangote ke zargin akwai wasu daga cikin manajojin da ke yi musu kwange a wajen biyansu hakkokinsu, lamarin da ya yi sanadiyyar suka tsunduma yajin aiki na sai baba ta gani.

1 Comments

  1. Kwarai kuwa managogin suna musguna masu kwarai da gaske

    ReplyDelete
Previous Post Next Post