EFCC ta musanta raba kudaden da ta kwace hannun Emefiele


Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta musanta rahotannin da ke cewa jami’anta sun raba wasu kadarorin da aka kwato daga tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele da mukarrabansa.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba, ya musanta rade-radin da ake ya dawa a kafar sada zumunta ta zamani.

Hukumar ta ce wata jaridar yanar gizo ce mai suna Sahara Reporters ta wallafa, inda ta yi zargin cewa N54bn tayi batan dabo tsakanin wasu ministoci da mataimakan Shugaba Tinubu tare da hadin gwiwar jami’an EFCC.

Post a Comment

Previous Post Next Post