Dokar shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba, za ta fara aiki mako mai kamawa - FG


A watan Yuli, Gwamnatin Tarayya ta amince da wani tagomashin kwanaki 150 da ba za a caji haraji ba wurin shigo da masara, shinkafa, da alkama a matsayin wani mataki na yaki da hauhawar farashin abinci a fadin kasar.

Wannan doka dai kamar yadda shugaban hukumar ta Kwastam ya sanar, za ta fara aiki a mako mai kamawa.

Da ya ke magana a taron shugabannin hukumomin tsaro a Abuja, Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce za a fara aiwatar da wannan dokar ta shigo da wadannan kayan abinci da zarar an gama shirye-shiryen da suka dace.

Bashir ya kuma yi kira ga 'yan Nijeriya da su dan kara hakuri inda yace wasu daga cikin wadannan kayayyaki da za a shigo da su yanzu haka za su wuce ba tare da haraji ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post