Daliban da suka kai jami'ar Al-Qalam Katsina kara, sun yi nasara, har an ci tarar jami'ar N1m


Babbar kotun jihar Katsina ta umurci hukumar gudanarwar jami'ar Al-Qalam da ke Katsina da ta ba tsoffin dalibanta biyu Hawwa'u Sani Barda da Rabi'atu Sani Barda sakamakon kammala digirinsu.

Kazalika, kotun ta umurci hukumar gudanarwar jami'ar da ta lamunce wa wadannan dalibai zuwa shirin yi wa kasa hidima biyo bayan kammala karatun digiri da suka yi a jami'ar.

Bugu da kari, kotun ta umurci hukumar gudanarwar jami'ar da ta biya tsoffin daliban tarar kudi Naira milyan daya saboda bata musu lokaci da ta yi wajen sanya su cikin shirin yi wa kasa hidima na NYSC bisa zargin da jami'ar ta yi musu cewa ba su biya kudin rajista ba na zangunan karatu hudu.

Daliban, 'yan'uwan juna, sun maka jami'ar Al-Qalam Katsina kotu, inda suke kararta kan hana su sakamakon kammala digiri da kuma kin sanya su cikin shirin yi wa kasa hidima na NYSC.

Jami'ar Al-Qalam Katsina, jami'ar mai zaman kanta ya zargi daliban, Hawwa'u Sani Barda da Rabi'atu Sani Barda da Hafsat Sani Barda da cewa ba su biya kudin rajista na jami'ar ba na tsawon zangunan karatu hudu, zargin da daliban suka musanta.

Da yake yanke hukunci, Mai Shari'a Abbas Bawale, ya ce bayan sauraren hujjojin da lauya ya gabatar, kotu ta gano cewa Hafsat Sani Barda da Rabi'atu Sani Barda sun biya kudin rajistar karatunsu na tsawon zangunan karatu hudu.

Alkalin ya ce hukumar gudanarwar jami'ar Al-Qalam Katsina ta gaza gamsar da kotu cewa wadannan dalibai ba su biya kudin rajista ba.

1 Comments

  1. Masha Allah alhamdillah gaskiya tabayyana nima inanan zuwa

    ReplyDelete
Previous Post Next Post