Asusun NELFUND na gwamnatin Tinubu ya bai wa daliban jami’o’i 6 tallafin N20,000 ga kowane dalibi 20,000

Asusun ba da bashin karatu na Nijeriya NELFUND ya sanar da ba da wani hasahin N20,000 ga dalibai 20,371 a jami'o'i na kasar nan na watan Juli, 2024.

Daraktan kudi na asusum Mr Ibom Uche ya sanar da hakan a ranar Litinin a wata sanarwa da ya fitar.

Ibom Uche ya lissafto jami'o'in da suka hada da jami'ar Bayero, Kano, jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, jihar Katsina, Jami'ar Ilori, jihar Kwara, Jami'ar Benin jihar Edo, jami'ar Ibadan jihar Oyo da jami'ar Maiduguri a jihar Borno.

Daraktan ya ce wannan ya nuna karara irin zuar Shugaba Tinubu na ganin ya tallafi dalibai domin su cika burikan da suka sa a gaba a fadin kasar nan.

Ya ce wannan asusu na aiki domin ganin ya raba wa dalibai wannan hasahi daga karin jami'o'i 55 na kasar nan domin su ma su amfana.

Post a Comment

Previous Post Next Post