Dakatar da biyan harajin kayan abincin da ake shigowa da su daga waje zai rage farashin kayayyaki a Nijeriya - Shugaban Kwastam
Shugaban hukumar hana fasa kwauri a Nijeriya Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce dakatar da haraji kan kayan abinci da magunguna da ake shigowa da su daga kasashen waje zai rage farashin kayan abinci.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wani taron ganawa da shugabannin tsaro a Abuja kan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na rage farashin kayan abinci.
Yace an shirya zanga-zanga ne akan abubuwa da dama, daya daga cikinsu shine kawo karshen hauhawar farashin kayayyaki",Mun gano cewa ana shigo da abinci mai tarin yawa da ake amfani da shi a Najeriya. Don haka daya daga cikin abubuwan da shugaban kasa ya yi na rage tasirin farashin shigo da kaya shi ne dakatar da harajin kwastam da haraji kan kayan abinci da ake shigowa da su na wani lokaci.
“Mun yi imanin cewa idan aka aiwatar da hakan, zai taimaka wajen rage farashin kayayyakin abinci a kasuwanni.