Da ba a shafa wa Yahaya Bello da El-rufa'i kashin kaji ba, da sun tausashi zukatan masu zanga-zanga a arewa - Jigon APC

Wani mamba na kwamitin yakin neman zabe na shugaba Tinubu a jam'iyyar APC a zaben da ya gabata, Jesutega Onokpasa ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai a matsayin wandanda tuni za su tausashi zukatan masu zanga-zanga a yankin Arewa, ba domin an sha masu kai da tuhume-tuhume marasa tushe ba.

Jesutega ya kuma kara da cewa tsofaffin gwamnonin za su ɗauki gabarar magana a madadin shugaban kasa Bola Tinubu cikin wani salo domin su kwantar da hankulan mutane tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Onokpasa ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo wanda ya ke sukar masu mukamai da 'yan arewa a gwamnatin shugaba saboda zarginsu da rashin ɗaukar wani mataki don kare gwamnatin Tinubu tare da tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin masu zanga-zangar ƙasa baki ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post