Ban yi almubazzaranci da kudin da na samu daga wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf ba– Zainab Ado Bayero

Ban yi almubazzaranci da kudin da na samu daga wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf ba– Zainab Ado Bayero 

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayi sarkin Kano, Zainab Jummai Ado Bayero, ta karyata ikirarin da ake na cewa ta yi almubazzaranci da kudaden da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya baiwa ita da mahaifiyar ta tare da dan uwanta.


A watan Yunin wannan shekarar ne dai, Jummau ta fito ta bayyanawa jama'a neman tallafin kudi, a lokacin da ita tare da mahaifiyarta da yayanta, ake yi musu barazanar kora daga wani gida a Legas sakamakon rashin biyan kudin haya.


A cewar Zainab, ‘yan uwanta sun shiga mawuyacin hali tun bayan rasuwar mahaifinsu da suka hada da rashin wurin kwana da kudin da za su ci gaba da karatunsu.



Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce ya ziyarce su a Legas ne a ranar Talata 25 ga watan Yuni, 2024 bisa umarnin gwamnan domin ganawa da Manajan gidan da iyalan Ado Bayero suka zauna, Mista Sunel Kumar tare da biya musu kudin.


Zainab wadda ta godewa gwamnan bisa wannan karimcin, rahotanni sun bayyana cewa, daukar matakin ya zo ne a daidai lokacin da aka shirya wasu matasa domin su kore su daga gidan saboda sun kasa biyan kudin hayar.


Sai dai bayan wata biyu jummai Bayero ta sake fitowa neman taimako, inda ta roke su cewa suna bukatar karin kudi domin su samu biyan bukatunsu su mayar da dan uwanta makaranta.


Hakan dai ya haifar da cece-kuce inda wasu suka ce ta salwantar da kudaden da gwamnan ya aike mata da 'yan uwan ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post