Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan ya sanar cewa bai taba nada Bashir Hadejia wani mukami a cikin gwamnatisa ba kamar yadda ake yadawa.
Gwamna Dauda na magana ne a cikin shirin "One-on-One na gidan Talabijin na Channels, inda ya ce ko wasikar da ke yawo kan wannan batun, ba ta gaskiya ba ce, ba ta da tushe bare makama.
Gwamnan ya cigaba yana cewa a duk lokacin da zai nada wani mukami a gwamnatinsa, yana sanar da kafafen yada labarai.
"Na kalubalanci cewa ko ma wanene da ya fito ya nuna inda muka sanar da nada Bashir Hadejia." In ji Gwamnan Dauda Lawan.
Ya ce a saman faifai suke tafiyar da gwamnatinsu a jihar, babu wani nuku-nuku, illa siyasa ce kawai 'yan adawa ke neman yin amfani da ita domin shafa masa kashin kaji.