Bama cikin wadanda suka yi ƙone ƙone a zanga-zangar Kano-Ƙungiyar Kano Peace Ambassadors



Ƙungiyarnan ta Kano state Peace Ambassadors mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya ta nisanta kanta daga ƙone-ƙone da aka yi lokacin zanga-zanga da aka yi ranar Alhamis a Kanon.

Shugaban ƙungiyar Nasiru Usman Na'ibawa ya ce sun gudanar da zanga-zanga mai tsafta daga ofishin su da ke titin Aufu Baƙo zuwa fadar Sarki Sunusi, suka miƙa masa takardar koken jama'a.

Ya baiyana cewa sun so su mika wata wasikar kuma ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf amma shawarar da jami'an tsaro suka basu ya sa suka fasa.

Ya ce shugaba Tinubu yana bukatar ƙarin lokaci dan magance matsalolin ƙasar, yana kuma shawartar 'yan Najeriya suka tsãme kansu daga zanga zangar da ake domin ta fara haifar da ɗa mara ido.

Post a Comment

Previous Post Next Post