Babban bankin kasar Kenya ya rage kudin ruwa

A Talatar nan makon nan ne babban bankin kasar Kenya ya sanar da rage kudin ruwa na farko cikin shekaru huɗu.

Wannan na zaman wani yunkurin kawo saukin matsi da hauhawar farashi, yayin da ita kuma gwamnatin kasar ke gwagwarmaya don tara kudaden shiga da biyan bashin jama'a bayan zanga-zangar da aka gudanar kan karin haraji.

Kwamitin kula da harkokin kudi na kasar (MPC) ya bayyana rage kashi daya bisa hudu na kudin ruwan zuwa 12.75 cikin dari.

A cikin wata sanarwa da gwamnan babban bankin kasar kuma shugaban kwamitin (MPC)ya fitar ta ce wannan mataki da aka dauka a baya ya rage hauhawar farashi gaba ɗaya, ya kuma daga darajar kudin kasar sannan ya shawo kan matsalar hauhawar farashin kayan abinci.

Kazalika, jimillar hauhawar farashin kasar na shekara zuwa shekara ya ragu daga 4.6 zuwa 4.3.

Post a Comment

Previous Post Next Post