Ba mu samu umurnin biyan N70,000 ga masu bautar kasa ba - Hukumar NYSC
Hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC ta ce har yanzu ba su samu umurnin kan ko za su biya 'yan bautar kasa mafi karancin albashi na N70,000.
Hukumar NYSC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Mista Eddy Megwa ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Gwamnatin Nijeriya dai ta riga ta sanar da N70,000 a matsayin mafi karancin abin da za a iya biyan karamin ma'aikaci a fadin kasar.