Ba mu kayyade farashin litar fetur dinmu ba - Matatar man Dangote

Hukumar gudanarwar matatar man Dangote ta musanta batun kayyade farashin litar man fetur.

Babban jami'in sashen sadarwa na kamfanin Anthony Chiejina, ya sanar da hakan yayin da yake mayar da martani ga wani rahoto kan hasashen 'yan kasuwa na sayar da litar fetur din kan kudi N600 na man Dangote da aka wallafa a jaridar Punch a ranar Talata, 13 ga Agusta, 2024.

Chiejina ya bayyana cewa kungiyar 'yan kasuwan man fetur ta Nijeriya ba abokan kasuwancinsu ba ne har yanzu. Ba kuma su taɓa tattauna batun farashin Man Fetur da su ba, kuma ba su da wani izini ko iko na magana a madadinsu, ko da ko wacce irin manufa.

Kazalika, sanarwar ta bukaci jama’a da su yi watsi da wannan magana mara tushe. Ta kuma kara da cewa suna da hanyoyin sadarwa na hukuma da suke amfani da su wajen bayyana ra’ayoyinsu ga masu ruwa da tsaki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp