Atiku ya caccaki Tinubu kan batun tallafin man fetur

Atiku ya caccaki Tinubu kan batun tallafin man fetur 

Madugun adawa a Nijeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abu bakar ya caccaki shugaba Bola Tinubu kan rahotannin sake dawo da tallafin man fetur.


Atiku ya mayar da martani ne kan rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa shugaban kasar ya umurci kamfanin mai na kasa(NNPCL) da ya kashe kudaden da hukumar ta ke samu kan tallafin mai.


Rahoton ya ci gaba da cewa, ana sa ran kamfanin na NNPC zai dakatar da biyan kudaden na tsawon watanni takwas a wannan shekara - daga watan Mayu zuwa Disamba domin biyan tallafin.


Da yake mayar da martani, Atiku a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X a ranar Litinin, ya bayyana matakin a matsayin boyeyyen sirri,da ba kowa ya sani ba.


Ya ce, saboda sahihan bayanan da ke yawo ta kafafen yada labarai dangane da yadda gwamnatin tarayya ta ci gaba da bayar da tallafin da ake bayarwa a kan Premium Motor Spirit (PMS) a boye, ya nuna wani babi na rashin gaskiya a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

1 Comments

  1. Mudai fstanmu a najeria Allah ya bamu yadda zamuyi Amin summer Amin

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp