APC ta yi tir da harin da aka kai sakatariyar jam'iyyar a Zamfara
Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da masu zanga-zanga suka kai sakatariyar jam’iyyar ta jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Litinin.
Sanarwar tace jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da wasu bata-gari da suka kai hari a yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa.
"Ko a ranar juma’ar da ta gabata, jam'iyyar APC ta gargadi gwamnatin jihar kan yadda ta bar wasu bata gari suna huce haushin su kan APC da shugabannin ta.
Yace a kwanakin nan wasu bata gari sun yi amfani da zanga-zanga wajen kai hari gidan Sen. Sahabi Ya’u a Kauran Namoda da kuma yunkurin rusa gidan tsohon Gwamna Bello Matawalle da ke Gusau.
Ya kuma ce jam’iyyar ta kuma roki jami’an tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.
"Babban abin bakin ciki ya faru ne a Litinin, yadda bata gari da sunan zanga-zanga suka mamaye Sakatariyar jam’iyyar APC da ke kan titin Sokoto Bye Pass Road, Gusau, tare da lalata wuraren da suka hada da gilasai da kofofi da kayan ofisoshi tare da kwamfutoci da aka kwashe a ofisoshin.
Yayi kira mambobi da magoya bayan jam'iyyar da masu fatan alheri da su ci gaba da kasancewa cikin masu bin doka da oda dan samun zaman lafiyar jihar