APC ta kira taron NEC domin fara shirin zabo sabon shugaban

Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da ranar 12 ga watan Satumba domin gudanar da taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
Taron kusoshin jami'iyyar na NEC shi ne na biyu mafi girma wajen yanke hukunci ga babban taron jam’iyyar.

Mataimakin sakataren jam’iyyar APC na kasa Barista Fetus Fuanter ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa (NWC) a Abuja, ranar Alhamis.

Fuanter, wanda ya kasance tare da sauran mambobin kungiyar NWC yayin taron manema labarai ya kuma bayyana cewa mambobin jam’iyyar APC na kasa za su yi taro a ranar 11 ga watan Satumba, kafin taron na NEC.

Post a Comment

Previous Post Next Post