Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya Kawu Sumaila ya ce a duk wata yana yana samun jimillar kudi Naira milyan 21.
A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, ta jiyo Sanata Kawu Sumaila na cewa albashin Naira milyan daya da hukumar tattarawa da rarraba kudaden shiga ta kasa ta ce ana ba Sanatoci, ta ragu zuwa N600,000, amma akwai alawus-alawus da ake biya da suka kai Naira milyan 21 ga duk kowane Sanata.
Sanata Kawu Sumaila ya yi magana ne sa'o'i 24 bayan da hukumar da ke da alhakin kayyade albashin masu mukaman siyasa ta fito karara ta sanar cewa albashin kowane Sanata bai wuce N1m ba.
Sai dai Sanatan ya ce da jimillar wadannan kudade ne kowane Sanata ke amfani yana tafiyar da lamurran ofishinsa.