An saki yan kasar Poland da aka kama sun daga tutocin Rasha yayin zanga-zanga a Kano
An saki wasu daliban kasar Poland da aka kama a Naijeriya yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a ranar Laraba.
A farkon wannan wata ne Najeriya ta ce ta kama wasu 'yan kasar Poland bakwai da suka daga tutocin kasar Rasha a lokacin zanga-zanga a jihar Kano.