An saki Bobrisky daga gidan gyaran hali na Kiri-kiri


Sannannen mai sha'awar shiga irin ta mata din nan Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya shaki iskar 'yanci bayan da ya fita daga gidan gyaran hali na Kiri-kiri a Litinin din nan.

Bobrisky dai ya kwashe watanni 6 tsare a gidan yari bayan da kotu ta kama shi da laifin 'likin' kudi na irin na gadara a wajen wata walima.

A ranar 12 ga Afrilun, 2024 ne dai aka yanke wa Idris hukuncin daurin watanni 6 bayan da kotu ta same shi da wannan laifi na cin zarafin takardar Naira.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu'annati, EFCC dai ce ta maka Idris Okuneye kotu bayan da ta zarge shi da wulakanta Naira, kotun kuma ta same shi da laifin, ta yanke masa hukunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post