An kama dan shekaru 62 da ke buga jabun kudi a Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta sanar da kama Tahir Ahmad mai kimanin shekaru 62 da zargin buga jabun kudi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ahmad Wakili ya sanar da hakan a Bauchi, inda wata mota daga Jos ta taso zuwa Bauchi, ta tsaya a Tilden Fulani cikin karamar hukumar Toro, inda ta dauko Tahir Ahmad a matsayin fasinja aka nufa da shi zuwa Bauchi.

Sanarwar 'yan sandan ta ce ana cikin mota ne, mutumin ya fitar da wata takarda ya fara karanta wasu dalasimai, take ta koma kudi, Naira dubu daya. A cikin motar ne aka fara zargin cewa wannan kudin na 'samara' da mutumin nan ya yi a mota na jabu ne.

'Yan sandan suka ce daya daga cikin fasinjojin motar da aka isa Bauchi, ya garzaya ya sanar da 'yan sanda halin da ake ciki.

Ahmad Wakili ya ce bayan kamo mutumin, aka tsananta bincike a kansa, mutumin ya amsa laifinsa, 'yan sanda sun kuma samu jimillar kudi Naira dubu 238 a hannun mutumin a matsayin kudin jabu.

Post a Comment

Previous Post Next Post