An kafa cibiyoyin samar da lantarki a wasu manyan jami’o’in Nijeriya, in ji ministan makamashi

Gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar wutar lantarki sanya cibiyar samar da lantarki a manyan jami’o’i shida na tarayya, a matsayin wani yunkuri na samar da ingantacciyar wutar lantarki a muhimman bangarori ga al’umma.

Hukumar ta bayyana cewa ta samu gagarumin ci gaba wajen bunkasa ayyukan samar da wutar lantarki a Najeriya.

Wannan ya biyo bayan wata tattaunawa da daraktan hukumar, Abba Abubakar Aliyu, ya yi da ministan kudi kuma ministan tsare-tsare na tattalin arziki, Wale Edun.

Jami’o’in sun hada da jami’ar Abuja, jami’ar Maiduguri, jami’ar koyon dabarun aikin gona ta Michael Okpara da ke Umudike, jami’ar tarayya ta Gashua a Yobe, jami’ar ta tarayya da ke Abeokuta, da kuma kwalejin tsaro ta Najeriya da ke Kaduna.

Post a Comment

Previous Post Next Post