Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da janye dokar hana fita bakidaya a jihar bayan zanga-zanga tsadar rayuwa da aka gudanar da ta rikide ta koma tarzoma a wasu yankunan jihar.
A cikin wata sanarwa daga Samuel Aruwan da ke kula da ma'aikatar tsaron cikin gida na jihar, ta ce dama garuruwan Zaria da Kaduna ne aka sanya dokar biyo bayan hargitsi da aka samu a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, amma an janye bayan samun rangwamen wannan lamari.
Kazalika, jihar Jigawa ma ta sanar da janye dokar hana fita din bakidaya a kananan hukumomi 8 na jihar da aka kakaba biyo bayan tashin tarzoma a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Sagir Musa ya fitar, ta ce kananan hukumomin da aka sanya wannan doka a baya su ne Kazaure, Birnin Kudu, Gumel, Hadejia, Kiyawa, Babura, Roni da babban birnin jihar, Dutse.
Jihar Kano ma ta sanar da janye wannan doka bakidaya kamar yadda Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanar.
Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar janye dokar ne biyo bayan samun rahotannin ingancin tsaro a sassan da aka samu rahotannin tashin hankali a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.