An harbe wani dan kasuwa, tare kashe wasu 'yan sanda biyu a wani yamutsi da ya kaure tsakanin jami'an 'yan sanda da mabiya mazhabar Shi'a a kasuwar Wuse da ke Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, an harbi dan kasuwar mai suna Amiru na gudun ceton ransa, yayin da wani alburushi ya same shi a kirji, a lokacin da 'yan sanda ke korar masu zanga-zanga na mabiya mazhabar Shi'a a Wuse zone 6, Abuja.
Kazalika, bayanai sun ce an kone motocin 'yan sanda uku a yayin yamutsin.
Mabiya mazhabar Shi'a din dai na muzaharar Arbaeen don cika kwanaki 40 na bikin Ashura.
Haka kuma yan sanda sun kashe mana aboki wanda baiji bai gani ba hasalima dan kasuwar Wuse Market din ne
ReplyDeleteAllah Yajikansa Da Rahama 🙏 Amiru Tabbatar Mutunin Kirkine 🙏😰
ReplyDelete