An garzaya da wasu iyalai asibiti bayan sun sha wani kunu


Wasu bayanai da jaridar Daily Punch ta samo daga jihar Benue sun ce an garzaya da wasu iyalai asibiti bayan sun sha wani kunu a yankin Egba, cikin karamar hukumar Agatu ta jihar Benue.

Bayanan sun ce lamarin ya faru ne kan wata mata da ba ta da miji mai suna Amina da 'ya'yanta da wani jikanta, jimilla dai su shida ne aka ce sun sha wannan kunu da ya yi sanadiyyar cikinsu ya baci har aka garzaya da su asibiti.

Wani dan unguwarsu Amina ya shaida cewa iyalan sun fara zazzaga amai a gida bayan da suka sha kunun, daga nan aka garzaya da su asibiti.

Dan unguwarsu Amina de n ya ce lokacin da aka garzaya da su asibiti ba su san inda kansu yake ba saboda tsananin ciwo.

Post a Comment

Previous Post Next Post