An dakatar da sayar da shinkafa mai rangwamen kudi ga ma'aikatan gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin tarayyar Nijeriya dai ta ce a dakata da batun sayar da wannan shinkafa mai rangwamen kudi ta N40,000 ga ma'aikatan gwamnatin kasar.

Kazalika, gwamnatin ta kuma sanar da janye duk wata takarda wato circular da ta aike wa ma'aikatun gwamnati kan wannan batu na sayar da shinkafar a farashi mai rahusa ga ma'aikatan gwamnatin kasar da ke cewa duk maaikacin da ke bukata, ya nema a tsarin da aka ayyana.

Bayanin hakan na a wata sabuwar takardar da aka fitar daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati da jaridar Punch ta samu kwafi a Abuja.

Sanarwar mai dauke da kwanan watan 2 ga Agusta 2024, da Daraktan Ma’aikata na ma’aikatar, Aderonke Jaiyesimi ya sanya wa hannu, ba ta bayar da dalilin janye takardar farko ba.

Kazalika, ba a nuna ko an dakatar da shirin ne ko kuma an fasa kwata-kwata.

Tun da farko, ma'aikatar ta ce duk ma'aikatan da ke da sha'awa, su cika fom akan gidan yanar gizo kuma su mika shi ga daraktan kula da ma'aikatan gwamnati na ofishin shugabar ma'aikatan tarayya, don amincewa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp