An dage taron wakilan gwamnatin tarayya da aka shirya tare da malaman jami'o'i

 An dage taron wakilan gwamnatin tarayya da aka shirya tare da malaman jami'o'i

An dage zaman da ake shirin yi tsakanin gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da aka shirya gudanarwa a yau.


Ko da yake ba a bayyana dalilin dage taron ba, amma a yanzu ana sa ran gudanar da taron a ranar Laraba 28 ga watan Agusta.


Malaman jami’o’in gwamnati a karkashin kungiyar ASUU a makon jiya sun yi barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar saboda abin da suka bayyana a matsayin rashin goyon bayan gwamnatin tarayya na mutunta yarjejeniyar da aka sake kullawa a shekarar 2009.


Sanarwar dai na daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwar kungiyar, wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan a karshen makon da ya gabata.


Bukatun ASUU sun hada da harkokin jin dadin ma'aikatan, samar da kudade ga jami’o’i da kuma bukatar dakatar da yaduwar jami’o’i a fadin kasar nan.


Taron da aka shirya shi ne don hana sake yajin aikin ASUU.

Post a Comment

Previous Post Next Post