An biya naira biliyan 700 a matsayin cin hanci a Nijeriya a 2023 – ICPC

 


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta nuna takaicin ta kan yadda ake samun yawaitar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Shugaban hukumar Musa Aliyu ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da jami'ar Ahmadu Bello ta shirya.

A cewar sa kimanin Mutane miliyan 87 a Nigeria ke da hannu bumu-bumu da cin hanci da rashawa da suka Kai naira biliyan 700 da aka gano a cikin shekara ta 2023 inda a yankin karkara lamarin yafi yawa fiye da birane.

Shugaban ya ce cin hanci da rashawa shi ne babban cikas ga ci gaban Najeriya

Hukumar ta ICPC ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin dan Adam da inganta adalci a tsakanin al’umma ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa


Post a Comment

Previous Post Next Post