An bindige "DPO" a shingen binciken sojoji a jihar Zamfara


Babban jami'in dan sanda mai kula da ofishinsu na Wasagu wato DPO a jihar Kebbi ya rasa ransa ta dalilin harbin bindiga da ake zargin wani jami'in soja ya yi masa.

Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa Halliru Liman ya hadu da ajalinsa ne a wani shingen ababen hawa da sojoji suka kafa a yankin Dan Marke na karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce babban jami'in dan sandan na kan hanyarsa ta zuwa Kebbi don halartar wani taro. A kan hanyar ne sojojin da ke aiki a karkashin shirin Operation Hadarin Daji suka tsayar da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce sojojin sun bindige DPO din nan take duk kuwa da ya nuna musu shaidar cewa shi jami'in dan sanda ne.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan ya fitar a ranar Alhamis, ta ce rundunar 'yan sandan ta bukaci da a gudanar da kwakkwaran bincike don hukunta wadanda ke da hannu.


Post a Comment

Previous Post Next Post